Burkina Faso gwamnati ta yi gargadi
November 25, 2020Talla
Hakan kuwa ya biyo bayan sanarwar da 'yan adawar kasar suka bayyana na cewar an tafka magudi a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata wanda suka yi brazanar cewar ba za su amince ba da sakamakon zaben. A cikin wata sanarwa da minista yada labarai na Burkina Fason Remi Fulgance ya bayyana ya ce gwamnati ba za taba amincewa ba da tada zauna tsaye.