Burkina: Gwanmati ta kori Zida daga rundunar soji
December 30, 2016Yayin wani jawabi da ya yi, Shugaba Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso, ya kuma sanar da shirinsa na yin garan bawul ga majalisar ministocin kasar. Cikin canje-canjen da za a kawo, shugaban zai saki matsayinsa na ministan tsaro, tare da nada wani minista na musamman da zai kula da harkokokin tsaro a kasar a cewarsa, wanda tuni ya nada sabon babban hafsan hafsoshin kasar.
Shugaban na Burkina Faso ya sanar da wani zaman taro da zai gudana a watan Janairu mai kamawa, tsakanin kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, inda za su tattauna kan batun sa ido ga iyakokin kasashen ganin yadda ake dada samun kai hare-haren ta'addanci. A watan Janairu ne dai da ya gabata, Janar Isaac Zida ya samu zuwa wurin iyallansa da ke kasar Canada, bayan da ya samu takardar izini tafiya daga Shugaban kasar Mark Kabore, amma kuma wa'adin ya fice bai dawo ba.