1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina jam'iyyar MPP ta samu mafi yawan kujeru a Majalisa

Salissou BoukariDecember 3, 2015

Sakamakon zaben 'yan majalisun dokoki a Burkina Faso, ya nunar cewa jam'iyyar sabon shugaban kasar ce ta lashe kujeru a kalla 55 daga cikin 127 na kasar.

https://p.dw.com/p/1HGCu
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo/picture alliance/AA/Olympia de Maismont

Jam'iyya mai bi mata ita ce ta UPC ta Zéphirin Diabré wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar, wadda ta tashi da kujeru 33, ya yin da jam'iyyar tsofon shugaban kasar Blaise Compaore ke rike da kambun ta uku da kujeru 18. Sai dai tuni masu lura da al'ammuran siyasar kasar ta Burkina Faso ke ganin cewa dole ne sabon shugaban ya hada karfi da sauran kananan jam'iyyu domin ya samu kai ga rinjayan da ake bukata na 'yan majalisu 64 da za su bashi damar gudanar da ayyukansa yadda ta kamata. Tuni dai dama sabon shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré ya ce shi shugaba ne na dukkan 'yan kasar Burkina Faso kuma zai yi aiki tare da kowa cikin kasar.