Bukatar taron dangi a yaki da ta'addanci
May 16, 2019Talla
Ministan harakokin wajen kasar ta Burkina Faso Alpha Barry ne ya sanya wannan kira a taron da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan Alhamis kan halin da ake ciki a yankin na Sahel.
Minista Barry wanda ke magana da yawan kungiyar G5 Sahel a wurin wannan taro ya ce lokaci ya yi da ya kamata kasashen duniya su tashi su dauki mataki a yankin na Sahel kamar irin wanda suka dauka a Iraki da kuma Afganistan.
Ministan wanda ya zano jerin hare-haren da kungiyoyin 'yan ta'adda suka kaddamar a baya baya bayan nan a Burkina Faso da kuma Nijar ya fito fili ya shaida wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya cewa matsalar ta'addancin da ake fuskanta a yankin ta fi karfin kasashen kungiyar ta G5 Sahel kuna tana bukatar taron dangi.