1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta gargadi masu zanga zanga a Hong Kong

Abdullahi Tanko Bala
August 6, 2019

Wani babban jami'in gwamnatin Chaina ya gargadi masu zanga zanga a Hong Kong da cewa za su sanya kafar wando daya yayin da zanga zangar ke cigaba da yin kamari.

https://p.dw.com/p/3NQN2
Proteste in Hongkong
Hoto: Getty Images/AFP/A. Wallace

Chaina ta yi kashedin cewa lsaura kiris ta fara hukunta wadanda suka jagoranci zanga zangar rajin dimokradiyya da aka shafe watanni biyu ana yi a Hong Kong wadda ta rikide zuwa artabu da jami'an tsaro.

Kalaman wadanda suka fito daga Yan Guang mai magana da yawun majalisar gudanarwar yankin Hong Kong na nuna alamu cewa Beijin na shirin sanya kafar wando daya da masu zanga zangar kuma bata da niyyar tattaunawa kan bukatunsu ta neman garanbawul ga harkokin siyasa. 

Kawo yanzu dai Chaina bata shiga kai tsaye cikin lamarin ba duk da cewa ta sha aikewa da sakonni masu karfi a sharhunan da aka rika yadawa a kafofin yada labarai mallakar gwamnatin da ke yin Allah wadai da tarzomar da ta baiyana ta wasu tsageru.

Ko da yake hukumomin Hong Kong sun ce basa tsammanin akwai bukatar turo sojoji ko 'yan sanda daga Chaina domin taimakawa wajen kwantar da tarzomar, a yan kwanakin nan an ga wasu hotunan bidiyo na sojojin da 'yan sandan Hong Kong sanye da bakaken kaya suna atisaye a iyakar birnin Shenzen na tarwatsa gangamin masu zanga zanga