1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Shekaru 70 da mulkin kwamunisanci

Abdullahi Tanko Bala
October 1, 2019

Yayin da China ke bikin cika shekaru 70 da mulkin kwamunisanci a waje guda ta na fama da kalubalen siyasa da na tattalin arziki sakamkon takaddamar kasuwanci da Amirka

https://p.dw.com/p/3QXLY
Peking Parade 70 Jahre Volksrepublik China
Hoto: Reuters/T. Peter

China ta gudanar gagarumin biki don cika shekaru 70 da kafuwar mulkin kwamunisanci a Jamhuriyar kasar.

Shugaban Xi Jingping wanda har ila yau shine sakataren koli na jam'iyyar kwamunisanci ta China kuma shugaban hukumar sojin kasar tare da sauran shugabanni sun hallara a dandalin Tian'anmen inda suka kalli faretin soji.

A jawabinsa shugaba Xi yace suna matukar farin ciki da alfahari da wannan rana wadda ta hada kan dukkan al'umomin China na gida da waje tare da yiwa kasar su fatan alheri.

Yayin faretin, sojoji sun gwada cigaban da suka samu na makamai domin karfafa tsaron kasa.


Sai dai kuma kasar na fuskantar kalubalen siyasa da na tattalin arziki sakamakon takaddamar cinikayya tsakaninta da Amirka, lamarin da ya shafi safarar kayayyakin kasar zuwa kasuwannin duniya.