1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za gina haanyoyin mota da asibitoci a Ruwanda

Abdourahamane Hassane
July 23, 2018

Hulda tsakanin China da Ruwanda ta kama hanya bayan da Shugaban kasar China Xi Jiniping ya gana da Paul Kagame na Ruwanda a ziyara da ya kai a kasar.

https://p.dw.com/p/31xvq
Ruanda Besuch Präsident Xi Jinping China
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Shugaban kasar China Xi Jinping  ya saka hannu a kan kwangiloli kasuwanci guda 15 da gwamnatin Ruwanda inda ya kai ziyara a mataki na biyu na rangadin da yake yi a cikin wasu kasashen Afira. Kafin ranar Larba ya isa Afirka ta  ta Kudu inda zai halarci taron kasashe na kungiyar BRICS. A yarjejeniyar da shugabannin biyu na China da Ruwanda suka cimma China ta amince ta gina sabbin hanyoyin mota da asibitoci da kuma filin saukar jiragen sama a Ruwanda.