1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga sun yi nasara kan gwamnati

Ramatu Garba Baba
September 5, 2019

Shugabar gwamnatin Hong Kong ta ce gwamnatin China ta amince tare da bayar da goyon baya ga matakin da ta dauka a game da shirin janye dokar iza keyar masu aikata laifi kasar.

https://p.dw.com/p/3P23g
China, Hongkong: Carrie Lam
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Hanxin

Shugabar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam, ta ce gwamnatin China ta yaba da hukuncin da ta dauka na janye dokar don samar da zaman lafiya a kasar da ta fada cikin rudani tun bayan sanarwar gwamnati a game da shirin aiwatar da wata ayar dokar, da za ta bata damar iza keyar masu aikata laifi zuwa kasar ta China.

Ms Lam, ta fadi hakan ne a yayin da take wata ganawa a wannan Alhamis da manema labarai. A yammancin jiya Laraba ne Shugabar ta sanar da wanann mataki a cikin wani sako Bidiyo da ta wallafa bayan da ta ce rikicin ya jefa al'ummar kasar cikin damuwa.

Carrie Lam ta kuma yi kira ga masu zanga-zanga dasu yi watsi da hanyar tarzoma da kuma hawa tebirin sulhu da gwamnati. Daga bangaren gwamnati za su dauki matakan da suka dace a cikin sauri domin maido da doka da oda a cikin yankin.