1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta kafa dokokin tsaro a Hong Kong

May 28, 2020

Majalisar dokokin kasar China, ta amince da dokar nan ta sauya tsarin tsaro a yankin Hong Kong, matakin kuma da aka hakkake zai kawo wani babi na zanga-zanga a yankin.

https://p.dw.com/p/3cuEI
China Nationaler Volkskongress | Abstimmung Sicherheitsgesetz Hongkong
Hoto: Reuters/C. G. Rawlins

Dama manufar gaggauta wannan dokar da ta kafu a yau, ita ce kokari na danne karfin ikon majalisar yankin na Hong kong da kuma iya daukar mataki kan duk wani abu da ake ganin ya saba wa abin da China ke ra'ayi a can.

Gabanin wannan lokaci dai China sai da ta nanata kasancewa kan bakanta na amfani da sabon tsarin, sannan a gefe guda ta gargadi kasashen duniya kan su guji tsoma mata baki a harkokinta na cikin gida.

Masu sukar lamura da fafutukar kare hakkin jama'a, na cewa China na iya amfani da wannan dokar wajen cuzguna wa 'yan siyasan da ke da bambancin ra'ayi da ita a yankin na Hong kong.