China ta kakaba wa kamfanonin Amurka takunkumai
January 2, 2025Mahunkuntan China sun sanar da kakaba tankunkumi ga wasu kamfanonin Amurka guda 10 da shugabanninsu, saboda zarginsu da hannu wajen sayar wa tsibirin Taiwan da makamai.
Karin bayani: Chaina ta jaddada kudirinta na hade Taiwan
Takunkuman sun jibanci hana kamfanonin galibin su masu kera makamai shigar da kayayyaki ko fitar da su daga China da kuma haramta musu saka hannu jari a kasar, tare kuma da soke izinin shiga China ga shugabanni wadannan kamfanoni.
A cikin wata sanarwa da ta fidda a Alhamis din nan ma'aikatar kasuwanci ta China ta ce Bejing ta dauki wannan mataki ne da nufin kare martabar kasar da kuma tsaron al'ummarta.
Karin bayani: Sojojin China na gagarumin atisaye kusa da Taiwan
A baya-bayan dai China na yawaita gudanar da atisayen soja a kusa da Tsibirin na Taiwan wanda ta yi ikirarin cewa yankinta ne kuma ta dau alwashin dawo da shi karkashinta ko da kuwa ana ha maza ha mata.