1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta kama jami'in Kanada a Beijing

December 12, 2018

Kanada ta ba da belin babbar jami'ar China da ta ke tsare da ita dai dai lokacin da aka kama wani tsohon jami'in kasar a birnin Beijing.

https://p.dw.com/p/39uqs
Huawei
Hoto: picture-alliance/dpa/N. H. Guan

Kotun kasar Kanada, ta bayar da belin babbar jami'ar kamfanin nan na kasar China Huawei, wato Meng Wanzhou, bayan kwanaki da aka dauka ana tabka turanci kan rigimar da matar ta shiga da hukumomin Amirka.

Kotun ta ce matar ta tabbatar mata iya samunta ne a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, bayan daukar wasu matakai, ciki har da karbe mata fasfo.

Tun da fari dai madam Meng Wanzhou, ta bayyana fargaba kan halin lafiyarta muddin aka ci gaba da tsare ta har zuwa lokacin da ake son aika ta Amirka, kamar yadda aka so.

Kama matar dai ya dagula dangantakar diflomasiyyar China da kasar Kanada, kuma samun belin nata, ya zo ne 'yan sa'o'i bayan kama tsohon jakadan Kanada Michael Kovrig da aka yi a birnin Beijing na kasar China.