1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta jaddada goyon bayanta ga Shugaba Maduro

Zulaiha Abubakar MNA
February 9, 2019

Gwamnatin kasar China ta roki kasashen ketare su bar al'ummar Venezuwela su warware rikicin siyasa tsakaninsu da gwamnati.

https://p.dw.com/p/3D2nQ
Venezuela Krise | Präsident Nicolas Maduro in Caracas
Hoto: Reuters/Miraflores Palace

Wannan gargadi daga kasar China na zuwa ne jim kadan bayan kalubalantar wani taro da kasashen tuntuba 14 suka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata, karkashin jagorancin shugaban kasar Uruguay duk dai kan rikicin siyasar kasar ta Venezuwela.

A baya China wacce ta kasance mai goyon bayan Shugaba Nicolas Maduro ta ba shi bashin kudaden da yawansu ya kai Dala biliyan 60 don ya farfado da martabar gwamnatinsa.

Ko a watan da ya gabata ma'aikatar harkokin wajen China ta yi Allah wadai da matakin da Amirka ta dauka kan shugaba Maduro na amincewa da jagoran adawa Juan Guaido a matsayin shugaban rikon kwarya a Venezuwela.

 Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa da ke samun goyon bayan kasashen duniya kan batun shugabancin kasar duk kuwa da cewar Shugaba Maduro ya gargadi Amirka kan gudummawar kayan agajin da ta dauki aniyar kai wa al'ummar Venezuwela.