China ta soki Amirka kan karin kudin fito
April 4, 2018Talla
China ta yi kakkausar suka ga Amirka kan karin kudin fito da ya kai dala biliyan 50 akan kayayyakin da China ta shigar da su cikin kasar.
Chinan dai ta yi barazanar cewa ita ma a shirye take ta daukin ramuwar gayya.
Wannan gargadin dai ya fito ne daga ma'aikatar harkokin kasuwanci na China a cewar kamfanin dillancin labarain kasar Xinhua yayin da kasashen biyu ke ci gaba da jayayya kan harkokin kasuwanci.
A ranar Talata shugaban Amirka Donald Trump ya kara rura wutar takaddamar bayan da ya dora karin haraji na kashi 25 cikin dari akan kayan da China ta shigar da su kasar wanda kudinsu ya kai dala biliyan 50 domin martani ga matakin China wadda ta kara haraji kan kayayyakin Amirka.