China ta zayyana mafita kan rikicin Myanmar
November 20, 2017Kasar China ta bayyana matakai uku da za su taimaka a kai ga samun mafita a rikicin kasar Myanmar da 'yan kabilar Rohingya ke ganin tasku, farawa da shirin tsagaita wuta ta yadda 'yan gudun hijira a Bangaladash za su koma gida. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China ta bayyana haka gabannin tattaunawar jami'ai daga Tarayyar Turai da jami'ai daga yankin Asiya a zaman da za su yi a Myanmar ranar Litinin din nan.
Fiye da 'yan kabilar Rohingya dubu 600 ne suka tsallake zuwa Bangaladash tun a karshen watan Agusta bayan da sojoji suka kaddamar da farmaki a kansu a jihar Rakhine. Ministan harkokin wajen na China Wang Yi ya ce dole bangarorin biyu su zauna teburi guda kuma dole a samar da tsari na tsawon lokaci da zai kawar da talauci ga al'ummar yankin, talaucin da a cewar Yi ke zama tushen rikici tsakanin wadannan al'umma a kasar ta Myanmar.