1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Za mu kare martabar yankunan kasarmu

Abdullahi Tanko Bala
June 2, 2019

A wani lamari na tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro ministan tsaron China ya yi barazanar kasarsa za ta dauki matakin soji don kare muradun China kan Taiwan na hadewar China kasa daya dunkulalliya

https://p.dw.com/p/3JcTQ
Der chinesische Verteidigungsminister, General Wei Fenghe
Hoto: picture-alliance/AP/Y. Teck Lim

Ministan tsaron China Wei Fenghe a yau Lahadi yace kasarsa ba za ta jingine yiwuwar amfani da karfin soji game da batun hadewar Taiwan da sauran yankunan China ba.

"Yace wajibine China ta kasance kasa daya dunkulalliya. Dole ne mu tabbatar da haka. Wane dalili ne zai sa hakan ba zai yiwu ba? Idan wani ya yi kasadar neman raba Taiwan da China, to kuwa sojojin China basu da wani zabi da ya wuce su yi yaki a kowane hali domin hadin kan kasa.

Janar din sojin ya yi wannan kalamin ne a wani taron koli na kwanaki uku a Singapore da ya hada manyan wakilan sojoji daga sassan duniya.

Kalamin na zuwa ne kwana daya bayan da mataimakin sakataren tsaron Amirka Patrick Shanahan ya yi jawabi a wajen taron inda ya gargadi China ta daina yin barazana ga kasashe makwabtanta.