China za ta sassauta dokar hana fita
March 24, 2020Hukumomi a China sun sanar da cewa za su sassauta dokar nan ta hana fita a yankin Hubei inda cutar coronavirus ta samo asali, yankin da aka shafe kusan watannin biyu karkashin wannan doka. Batun sassauta dokar zai fara aiki ne a ranar 8 ga watan Afirilu.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan nasarar da aka yi na kwanaki biyar ba tare da samun mutum daya da ya kamu da cutar ba.
A share guda kuwa ana samun wasu yankunan kasar ta China da cutar ke bulla a cikinsu, ganin yadda baki ke shigowa da su daga wasu kasashen.
A ranar 23 na watan Janairu ne, kasar ta China ta ayyana dokar ta-baci na ba sani ba sabo, a yankin Wuhan musamman, wanda hakan ya taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
A halin da ake ciki dai al'amura sun fara komawa yadda aka saba a kasar ta China.