Christian Kaboré ya yi rantsuwar kama aiki
December 29, 2015Talla
Sabon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré ya yi rantsuwar kama aiki da tsakiyar ranar wannan Talatar, tare da halartar shugabannin kasashe da dama na Afirka da suka hada da na Côte d'Ivoire, Mali, Nijar, Sénégal, da na Guinea.
Wannan biki ya kawo karshen mulkin rikon kwarya da aka gudanar bayan faduwar gwamnatin shugaba Blaise Compaore a karkashin shugaba Michel Kafando wanda ya ce hakan wata babbar nasara ce ga demokaradiyya da 'yancin al'umma.
Dan shekaru 58 da haihuwa, sabon shugaban kasar ta Burkina Faso ya yi kira ga 'yan kasar da su dukufa wajen sauya halayyarsu, domin a samu cimma nasarar bunkasa kasar tare da karfafa ma'aikatunta, da ci gaban demokaradiyya da 'yanci al'umma.