Ci gaban jiragen kasa a Afirka.
China na son bunkasa hanyoyin sufuri a ketare da kuma zuba jari mai yawa a Afirka yayin da nahiyar ke murnar dawowa harkar jiragen kasa.
Jirgi mai gudu daga Abuja zuwa Kaduna
Tun shekara ta 2016 aka samar da layin dogo daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya zuwa Kaduna a arewacin kasar. Gina layin dogon mai tsawon kilo-mita 187, an tsara zai ci kudi euro miliyan 800. Bankin tallafin safarar kayayyaki na China ya ba da rancen euro miliyan 450.
Shugaba Buhari a cikin jirigin kasa
Shugaba Muhammadu Buhari bako na musamman a tafiyar kaddamar da sabon jirgin kasa. Tafiyar ta dauki sa'oi biyu da mintuna 40. Farashin tikitin dai dai yake da Euro 3, taragun gama gari, Euro 4 da Centi 25 kuma ajin alfarma.
Jirgin cikin gari a Addis Ababa
A babban birnin Habasha akwai jirgi mota huta, tun a 2015 wanda rukunin kamfanin jiragen kasan China ya samar da tallafin bashin. 'Yan China na cikin ma'aikatan da ke tafiyar da jiragen da kuma gyara har zuwa 2020 lokacin da kamfanin jiragen kasa na Habasha zai karbi ragama.
Hade Kudancin Afirka da hanyar sufuri
Kimanin 'yan Kenya 25,000 da ma'aikatan China 3000 za su gina layin dogo mai nisan kilomita 472 tsakanin Mombasa da Nairobi. Aikin zai ci kudi Euro bilyan 3.6 kuma China za ta samar da fiye da kashi 90 cikin 100 na kudin. Daga baya za a hade wasu biranen gabashin Afirka kamar Kampala da Juba.
Tarihin jirgin kasa a Livingstone
Sufurin jirgin kasa a Afirka yana da tsohon tarihi. A shekarar 1856 aka kaddamar da layin dogo na farko a Iskandiriyya da kuma Alkahira. Jirgin wanda ya fara a karni na 20 har zuwa 1976 yana nan a Zambiya a yanzu, ana iya ziyara domin kallo a gidan tarihi da ke Livingstone
Durkushewa bayan mulkin mallaka
Layin dogo da dama a Afirka, kasashen mulkin mallaka suka gina. Jiragen na safarar kayan sarrafawar masana'antu zuwa gabar ruwa, daga nan ake dauka zuwa Turai. Yawancin hanyoyin sun bace. Ragowar abin da ake gani a wannan hoto na layin dogo ne da aka gina a 1914 tsakanin Swakopmund da tashar ruwan Walvis wanda aka maye gurbi da sabo 1980.
Za a iya fadada layin dogo na Afirka
A 2015 bankin raya Afirka a wani rahoto ya jaddada muhimmancin sufurin jiragen kasa a nahiyar. Yana ba da damar safarar kaya cikin sauki da rage sufurin motoci musamman a manyan birane. Rahoton ya yi suka kan rashin kyawun layin dogon wadanda yawanci suke yankin arewaci da kudanci amma kuma ba'a hade su da juna ba.
Tsoffin tashoshin jiragen kasa za su fardo?
A kasashe da dama na Afirka tattalin arziki yana ci gaba haka ma bukatar hanyoyin sufuri yana karuwa. Idan China da sauran masu ba da rancen kudade suka ci gaba da zuba jari, tsoffin tashoshin jiragen kasa kamar wannan da ke Addis Ababa za su farfado.
Afirka ta Kudu ta shimfida layin dogo
Shirin sufurin jiragen kasa na gunduma "Gautrain" ya hade biranen Pretoria da Johannesburg da filin jirgin sama mafi girma a Afirka. Za a fadada shi daga kilo-mita 80 zuwa kilomita 230 a shekaru 20 masu zuwa. Afirka ta Kudu ita ce ke da layin dogo mafi tsawo a nahiyar da tsawon kilo-mita 21,000. Sai Sudan 7251 da kuma Masar mai 5085.
Jirgin Faransa a tashar ruwan Tangier
Galibin jiragen kasa masu gudu na arewacin Afirka. A shekarar 2015 Moroko ta karbi jiragen da ta yi oda samfurin TGV. Yana tafiyar kilo-mita 320 cikin awa daya tsakanin Tangier da Casablanca maimakon awa 4 da minti 45. Nan gaba za a fadada layin dogon zuwa Aljeriya da Tunisiya.