1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makamai ya ragu a duniya

Abdourahamane Hassane
March 14, 2022

An ba da rahoton cewar cinikin makamai a duniya ya ragu kaɗan a cikin 'yan shekarun nan. Sai dai ya karu a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/48Srx
Indien I Aufrüstung I Militär
Hoto: Manish Swarup/AP/picture alliance

Cinikin makaman kamar tankunan yaki da jiragen yaki da na ruwa na karkashin teku ya ragu da kashi 4.6 cikin 100 ,daga shekara ta 2017 zuwa 2021 idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka gabata. A rahoton da ta bayyana na shekara, cibiyar binciken zaman lafiya ta Sipri da ke birnin  Stockholm ta ce a Turai cinikin makaman ya karu da kishi 19 cikin dari. Sai dai alkalluman ba su tabo batun yakin da ake yi ba a Ukraine a game da makaman da ake shigar da su a  kasar.