Ciyar da Somaliya gaba na buƙatar tallafin jama'arta
September 17, 2012A wata zantawa da ya yi gidan Radiyon DW, Emmanuel Kisangani ya ce kiran da tsohon shugaban Somaliyan ya yi na a tallafawa sabon shugaba ƙasar bayan da ya sha rantsuwar kama aiki wani abin yabawa ne duba da shan kaye da ya yi wajen sake neman kujerar shugabancin ƙasar.
Kazalika ya ce matakin na tsohon wata 'yar manuniya ce ta ƙoƙarin da 'yan ƙasar ke yi na ganin sun ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu musamman a siyasance a wani ƙoƙari na sake gina ƙasar.
'Ya ce kiran da tsohon shugaban ƙasar ya yi abu ne mai kyau, sai dai akwai banbanci wajen faɗin hakan da kuma abin da ke ransa to amma ga yadda jama'a ke kallo maganar ta sa a iya cewar ya aikewa Somaliya kyakkyawan saƙo saboda a baya a ji tsoron cewar ko za a samu matsala wajen zaɓen musamman daga bangaren wanda su ka sha kaye kazalika ana ganin cewar za su iya juyawa shugaban baya'.
To duk da cewar sabon shugaban na Somaliya Hassan Sheikh Mahmud ya samu goyon baya daga tsohon shugaba da ma yunƙurinsa wajen yin kira ga jama'a su tallafa masa, Mr. Kisangani ya ce akwai jan aiki a gaba shugaban duba da irin ƙalubalen da ya tarar da kuma waɗanda ka iya tasowa nan gaba.
Mr. Kisangani ya ce 'akwai ƙalubale da dama ga ƙasar da ta kai tsawon shekaru ashirin ba ta da gwamnati tsayayyiya. Mafi muhimmaci a cikinsu shi ne batun tsaro, idan ana samun barazana daga ƙungiyar Al-Shabab musamman ma dai a Mogadishu to fa dole a ce hakan wani naƙasu ne ga ƙoƙarin sake gina ƙasar. Baya ga haka akwai buƙatar kafa hukumomi domin kuwa in babu su to ba wani abu da za a iya yi wajen gudanar da aiyyuka'.
Bisa waɗannan ƙalubale da Mr. Emmanuel Kisanganin na cibiyar nazarin sha'anin tsaro da ke Afrika ta Kudu ya jero ne ya sayan shi cewar to fa kafin shugaban ya samu nasarar da ya sanya a gaba, ya zama wajibi ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da mutanen da ke da nagarta da kuma shauƙin ciyar da ƙasar gaba.
Ya ce 'ba zai iya yin aiyyuka shi kaɗai ba saboda haka dole ne ya fara da zaƙulo mutane da ke da tunani irin na shi, waɗanda za su taimaka wajen kafa hukumomi da kuma gudanar da aiyyukan da ya kamata a ce an yi. A takaice dai mafita ita ce sanya mutanen da su ka dace a wajen da ya dace'.
Da ya juya kan batun girka gwamnati kuwa musamman ma dai samar da majalisar ministoci, cewa ya yi ya ƙyautu shugaba Hassan Sheikh Mahmud ya yi aiki kafaɗa da ƙafaɗa da wanda zai naɗa a mastayin Priyiminstansa domin a gudu tare a tsira tare.
Ya ce 'dole ne ya yi aiki tare da Priyiministan da zai naɗa wanda shi kuma zai naɗa ministocin da za su dafawa shugaban ƙasar wajen gudanar da aikinsa. Kaga dole a ce an samu waɗannan abubuwan a ƙasa to amma fa abu mai muhimmanci da ya kamata a yi la'akari da shi, shi ne samar da kuɗaden da mutanen za su tafiyar da aikinsu saboda haka dole shugaban ya miƙa ƙoƙon bararsa ga ƙashen da kuma hukumomi na duniya domin su tallafa masa'.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman