Corona ta sake yaduwa a Turai
March 22, 2022Talla
Darektan hukumar lafiyar Reshen Turai Hans Kluge ya ce coronar ta sake yaduwa a karkashin nau'in BA2 a Jamus da Birtaniya da Faransa da Italiya da cikin wasu kasashen guda 18 na Turai. Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO ta ce a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an sami sabbin mutane sama da miliyan biyar da suka kamu da cutar, yayin da wasu sama da dubu 12 suka mutu a Turai.