Coronavirus na ci gaba da kisa a China
January 23, 2020Talla
Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta dakatar da matakin da ta so dauka, na bayyana sabuwar kwayar cutar nan ta Coronavirus da ta bulla a China, a matsayin wata barazana ga duniya.
A wata ganawar gaggawa da ta yi da kwararru, hukumar ta ce za a saurarin karin wasu hujjojin da za su tabbatar da kasancewar cutar a matsayin babban bala'i da ke bukatar mataki na gaggawa, kafin a kai ga tabbatar da ita a matsayin.
Wannan cuta ta Coronavirus dai tuni ta bazu a China inda ta kama mutum 444, 17 kuwa suka mutu. Haka nan ma cutar ta shiga kasar Amirka
Tuni dai hukumomin yankin da ta bulla a ciki wato birnin Wuhan, suka hana shiga da fitar jama'a, musamman ma zirga-zirgar jirage.