An baiwa cutar Coronavirus suna
February 11, 2020Talla
A sanarwar da ya rabawa manema labarai a Geneva, shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce "CO" a matsayin Corona "VI" a matsayin Virus sai "D" kuma a matsayin Dieseas watau cuta 19 kuma a matsayin shekarar da cutar ta bullo. Shugaban hukumar ya ce sun samar da wannan sunan ne domin kauce amfani da sunan Corona da ke da alaka da mutane da dabobbi dama yankuan wasu alumma.
Bugu da kari Ghebreyesus ya ce duniya ta dauki cutar a matsayin wata babbar makiyar kowa da kowa. Ya zuwa yanzu dai sama da mutum dari ne suka mutu sanadiyar cutar yayin da wasu da dama suka kamu da ita. An sa ran a nan da watanni goma sha takwas a samo maganin wannan annobar da ke nema ta zama ruwan dare gama duniya.