1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka sun kashe jagoran al-Shabaab

September 5, 2014

Ma'akakatar tsaron Amirka ta tabbatar da kashe shugaban kungiyar al-Shabaab Ahmed Abdi Godane a wani farmaki da sojojin Amirka suka kai a ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/1D7sw
Somalia Mogadischu Al-Shabaab Kämpfer ARCHIV
Hoto: Jan Grarup, Laif

A wannan Jumma'a Amirka ta tabbatar cewa an kashe jagoran sojojin sa kai na kungiyar al-Shabaab a Somaliya a wani farmaki ta sama da Amirka ta kai a farkon wannan mako. Gwamnatin fadar White House na daukar wannan a matsayin babban naushi ga ayyukan kungiyar al-Shabaab mai alaka da kungiyar al-Qaida. Wata sanarwa da gwamnatin Amirka ta fitar ta ce mutuwar Ahmed Abdi Godane babbar asara ce ga 'yan ta'adda a Afirka kuma ta nuna irin kwarewar aikin hukumomin leken asiri da na soji da kuma kwararru na Amirka. A ranar Litinin da ta gabata Amirka ta kaddamar da hare-haren hadin guiwa da jiragen saman yaki marasa matuka da kuma masu matuka a kan wani taron kwamandojin al-Shabaab. Da ma dai ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta sanya sunan Ahmed Godane a jerin manyan 'yan ta'adda takwas a duniya da ake nema ruwa a jallo.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman