1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Habasha sun kutsa cikin Somaliya.

July 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bupw

Dakarun Habasha a cikin motoci masu sulke, sun kutsa cikin harabar Somaliya yau inda suka kafa wani sansani kusa da mazaunin shugaban gwamnatin wucin gadin ƙasar. Tuni dai mayaƙan ƙungiyoyin isalama na birnin Mogadishu sun ƙarato zuwa wajen garin Baidoa, inda gwamnatin wucin gadin ke da cibiyarta. Wani kakakin ƙungiyoyin islaman, wadda a halin yanzu ke riƙe da mafi yawan yankunan kudancin Somaliyan, ya i kira ga Habashan da ta janye dakarunta. Kakakin, Sheikh Sharif Ahmed ya faɗa wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, ƙungiyarsa z ata ƙaddamad da jihadi, idan gwamnatin Habashan ta ƙi janye dakarunta.

Habashan dai ta ce za ta yi duk iyakacin ƙoƙarinta wajen kare gwamnatin wucin gadin ta Somaliya daga duk hare-haren da ’yan islaman ke niyyar kai mata.