Dakarun kasa da kasa a Somaliya
September 28, 2012
Sojojin kasar Kenya da ke cikin rundunar gamayar Afrika da ke kasar Somaliya,sun aukawa garin Kishmayo garin da ke matsayin sansanin mayakan kungiyar kishinn islama ta Al-shebab a wannan juma'ar. A lokacin da ya ke wa manema labarai bayani,kakakin rundunar tsaron kasar Kenya kanar Cyrus Oguna ya ce sojojin Kenya sun samu nasarar kwace garin daga hannun mayakan ba tare da sun fusdkaci wata mumunar turjiya ba. To saidai wani mai magana da yayun kungiyar ta Al-shebab Chekh Abdulaziz Abu Musab ya musanta kama garin inda ya ce lallai an samu wasu sojojin kasar ta Kenya da suka yi yukunrin shiga to saidai mayanknsu suka mayarda su baya.
Birnin na Kishmayo shi ne gari mafi girma a kudancin kasar inda masu kishin islaman ke samun kudaden shiga a dangane da hada-hadan kasuwancin gabar tekun yankin.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe