Dakarun Somaliya sun fatattaki mayaƙan kungiyoyin islama daga Baidoa.
October 9, 2006A ƙasar Somaliya, wasu rahotannin da muka na nuna cewa, dakarun gwamnati tare da ɗaurin gindin da suka samu daga sojojin Habasha, sun cim ma nasarar fatattakar mayaƙan gamayyar kotunan islama daga kewayen garin Baidoa, cibiyar gwamnatin wucin gadin ƙasar. Rahotannin sun ce ɗaruruwan sojojin Habashan da mayaƙan rukunan gwamnatin sun kutsa cikin garin Bur Hakaba yau da safen nan, abin da ya tilasa wa mayaƙan sa kai na kotunan islaman tserewa daga wannan yankin. Wannan dai shi ne karo na farko da mayaƙan islaman suka sha kaye a wani ɗauki ba daɗi, tun da suka fara kai farmaki a birnin Mogadishu da yankuna daban-daban na kudancin ƙasar. Firamiyan riƙon ƙwarya an Somaliyan, Ali Muhammad Gedi, ya ce burin mayakan islaman ne kai wa garin Baidoa hari. Ƙasashen Kenya da Habasha dai sun ce a shhirye suke su taimaka wa gwamnatin Somaliyan kare garin Baidoa idan aka kawo mata hari.