Burkina Faso: Mayar da kasar hannun farar hula
January 28, 2022Talla
Damiba ya kuma ce bangarori daban-daban za su hadu don samar da jadawalin sauyi a gwamnatance, yayin da a 'yan kwanakin nan gwamnatin soji ta yi kokarin samun goyon bayan shugabannin addinai da ma na farar hula.
Yayin da yake jawabin daga fadar gwamnatin kasar cikin shigar sojoji, Laftanat Kanal Damiba ya ce matsalar tsaro ne babban batun da za a sa a gaba. A 'yan kwanakin nan ne dai dakarun soji suka hambarar da mulkin shugaba Roch Marc Kabore, bayan zarginsa da rashin yin katabus kan matsalolin 'yan tada kayar baya da kasar Burkina Fasi ke fuskanta.