Dan Adam shi kan janyo hamada
Kishi daya bisa uku na doron duniya na a kan hamada. Abin da kan janyo karuwar koma baya a kan sha’anin muhali. Yawan sare dazuzzuka na janyo gurgusowar hamada. Fadakarwa a ranar kare muhali ta duniya.
A kan kirkiro hamada
Wani lokaci dorina da giwaye sun rayu a cikin Sahara. Sai dai a yau Sahara ta kasance bushe kau. Sai wani dan karamin tafki wanda ruwan sama da ya sauka da ruwan karkashin kasa ke kwararra a ciki. Yanayi ya canza ta yadda hamadar ta kara zama yashi. Dan Adam shi ne ke da laifi.
Mutum ke lalata yanayi
Hamadar da aka kirkiro ta kan zama hamada, lokacin da dan Adam ya lalata yanayi a yankunan da ke da fari. Shuke-shuke na bacewa kasa ta mutu ba ta da albarkar noma. A lokaci guda kuma irin wannnan yanayi na hamada a kan samunshi kishi 70 cikin dari a wuraran da ake da kanfar ruwan sama kamar nan a Indiya.
Barazana ga duniya
Kowace shekara kilomita 70.000 na filaye ke zama hamada. Misali kamar girman Ireland. A cewar cibiyar raya kasashe ta Jamus(GIZ) kishi 40 cikin dari na yawan al’ummar Afirka na fuskantar barazanar gurgusowar hamada, kishi 39% a yankin Asiya da kuma kishi 30% a Amirka ta Kudu. Amma kuma da yankuna kamar nan a Amirka ko Spain dukkaninsu suna fuskantar barazana.
Hamada saboda yawan amfani da dazuzzuka
Yawan karuwar al’umma a cikin wasu kasashe shi ne dalilin karuwar hamadar. Misali a China kasar noman da daman take bushe na zaman abin dogaro na rayuwar al’umma. Ga dabobi da ke amfani da ciyawa shi ma wani dalili na janyo hamadar. Kana ga ruwan sama da iska da ke zaizeye kasa. A China a kowace shekara kilomita 2500 na filaye ne ke komawa hamada.
Tafki ba ruwa
A tafkin Aral a kan iyaka tsakanin Kazastan da Uzbekistan nan wata alama ce ta rashin nasara da aka gaza cimma wajen daidaita sh’anin noma abin da ya janyo hamada. A da tafkin Aral shi ne na hudu wajen girma a duniya. A yau ya ja baya. Tun lokacin Tarrayar Soviet kasashen biyu sun rika amfani da tafkin domin ban ruwa a cikin gonakin kada. Tun lokacin kuma jiragen ruwa sun daina kai da kawo.
Dazuzzuka sun koma wurin yawan bude ido
Kasashe masu tasowa ba su ka dai ba ne ke fama da fari. A spain hamada na ci gaba da gurgusowa. Saboda gine-gine da aka yi don masu yawan bude ido ta hanyar sare dazuzzuka don gina otel-otel. Yankin Guadalajara kusa da Madrid lamarin ya shafeshi.
Hamada wurin gujewa
Bayan gurbata lamarin muhali, hamadar na haddasa matsaloli. Al’umma na talaucewa, ba sa samun abinci isashe,dole su bar matsugunasu. A Afirka Hamada na janyo matsaloli a kan mutane miliyan 485 a cewar (GIZ). Majalisar Dinkin Duniya na sa ran sama da mutane miliyan 60 za su fice daga yankunan hamada a Afirka kafin nan da shekarun 2020
Yaki da hamada
Wasu kasashen sun kudiri aniyar yakar hamadar. Tun shekaru da dama China na kokarin yaki da hamadar ta hanyar shuka itace. A karkashin wani shirin na yin dashen itatuwa a wani filin da girmansa zai kai girman Kasar Jamus kafin nan da shekara ta 2020. Majalisar Dinkin Duniya na yin amfani da ranar muhali ta duniya (17-06-19) domin jan hankalin al’umma a kan matsalar hamada.