Dubban 'yan Afirka sun mutu a teku a 2024
December 27, 2024Kungiyar da ke kare hakkin bakin haure ta kasar Spain Caminando Fronteras ko kuma Walking Boarders, ta ce 'yan kasashen Afirka su dubu goma da 547 ne suka mutu a bana a tafiyar kasadar da suka yi ta tekun Bahar Rum.
Haka nan ma a cewar kungiyar daga cikin adadin akwai wadanda suka ɓata ba tare da an gano su ba.
Kungiyar ta Caminando Fronteras ta kuma dora alhaki kan hukumomin kasar Spain, da ta ce sun fifita kare iyakokinsu maimakon ceto bakin hauren.
Galibin bakin haure da ke fitowa daga kasashen Afirka bakar fata da ke bi ta Spain dai, kan bi ne ta tsibirin Canary a kokarin shiga nahiyar Turai ala kulli halin.
Kididdiga dai ta nunar da cewa akwai sama da bakin 'yan ci rani sama da dubu 57 da 700 da suka isa Spain din daga farkon shekara zuwa ranar 15 ga wannan wata na Disamba, abin da ya nuan karin kashi 12% daga wanda aka gani a bara a daidai wannan lokaci.