1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan kudaden da ake kashewa wajen sayen kayan yaki ya karu

Abdourahamane Hassane
February 15, 2020

A rahoton da ta bayyana gabannin soma taron birnin Munich a kan sha'anin tsaro wata cibiyar bincike IISS ta ce yawan kudaden da ake kashewa wajen sayen kayan yaki ya yi haurawar da bai taba yi ba.

https://p.dw.com/p/3XoKX
Rheinmetall AG Düsseldorf Radpanzer Boxer
Hoto: Rheinmetall AG

Rahoton ya ce a cikin shekaru goma ba taba ganin irin haurawar ba ta yawan makamai a duniya. Kasashen Amirka da China na kan gaba a sahun kasashen da suka fi kashe kudade a harkokin soji wajen sayen makamai. Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a lokacin bikin bude taron ya ce a kwana a tashi duniya na yi nesa da irin alkawarin da aka dauka na samar da zaman lafiya sakamakon yake-yake da tashin hankali da duniyar ke fuskanta.