1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dutse na ci gaba da aman wuta a Kwango

May 27, 2021

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango sun bada umurnin kwashe wani bangare na al'ummar garin Goma saboda fargabar ci gaban aman wuta da dutsen Nyiragongo ke yi.

https://p.dw.com/p/3u1j3
DR Kongo Ausbrauch Nyamulagira Vulkan
Hoto: Steve Teril/AFP/Getty Images

Aman wuta daga dutsen Nyiragongo dai ya fara ne tun karshen makon jiya. A cewar gwamnan soji na yankin, lamarin ya sha gabansu a don haka ne ya zama wajibi su yi jigilar kwashe al'umma. Gwamnan ya kuma shawarci al'umma da su dauki abubuwan da za su masu amfani ne kawai don samun damar kwashe dukkan jam'a.

Alkalumman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na nuna cewa kimanin mutum 32 ne suka rasa rayukansu kawo yanzu yayin wasu 40 suka yin batan dabo, kana ana fargabar wasu fiye da dubu 5 su rasa matsugunninsu.