Ebolar Rogo ta bulla a yammacin Afirka
July 8, 2018Cutar da tuni masanan suka kira da Ebolar rogo na haddasa mutuwar dashen rogo da kashi 90 cikin 100 idan ta kama wanda ake ganin wata babbar barazana ce ga kasashen na Yammacin Afirka, inda a kullu yaumin ake kara samun bukatu na abinci, kuma rogo na daga cikin abincin yau da kullum a kasashe da dama na Afrika.
Bincike ya nunar cewa kashi 80 cikin 100 na al'ummar Najeriya miliyan 180 na amfani da rogo ko garin rago a gidajensu, yayin da a kasashe irin su Côte d' Ivoire, Burkina Faso da ma Mali, batun wani abinci da ake kira attiéké da ake yinsa da rago batu ne da ya zama ruwan dare a gidajen al'umma.
A shekara ta 1990 da wannan cuta ta rogo ta bulla a kasar Yuganda, yunwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3000 a wannan kasa a cewar Docta Pita jagoran tsarin nan na yammacin Afirka mai kula cutukan da ke da saurin yaduwa.