ECOWAS na taro kan juyin mulkin Nijar
July 30, 2023Talla
Gargadin nasu na zuwa ne yayin da shugabannin kasashen yammacin Afirka ke shirin yin wata ganawar gaggawa a Abuja, babba birnin Najeriya domin tattauna batun mataki na gaba da za su dauka da nufin matsa lamba ga sojoji su mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya.
Ana sa ran, shugabannin mambobin kasashe 15 na kungiyar ECOWAS da kuma kungiyar kasashe masu amfani da kudin CFA su dakatar da Nijar daga zama mamba a kungiyoyin, tare da sanya takunkumin cinikayya da ma rufe iyayokin kasashensu da ita.
Ana kuma sa ran kasar Chadi da mamba ba ce a cikin kungiyoyin ta halarci taron. Juyin mulkin Nijar dai na ci gaba da shan Allah wadai daga kasashen ciki da wajen nahiyar Afirka tare da yin watsi da duk wani shugaba da ba Mohamed Bazoum ba.