ECOWAS: Ta'addanci na ci mana tuwo a kwarya
December 22, 2018Kama daga Togo da Guinea Bissau inda ake kokarin kaucewa rigingimu na siyasa, ya zuwa ga Jamhuriyar Niger da aka kai ga rufe wasu makarantu dama ita kanta tarrayar Najeriya da kuma Senegal dake fuskantar zabuka cikin watanni biyun dake tafe dai, faduwar gaba dama karatu na rashin tabbas ne ke neman mamaye daukacin yankin yammacin Africa na ECOWAS.
Abun kuma da ya dauki hankallin shugabannin kasashen yankin da suka kammala taron kwana guda a Abuja suka kuma ce suna shirin daura damara domin tabbatar da kai karshen matsalolin tsaro da tabbatar da ingantaccen zabe a yankin.
Shugabannin kasashen Shida sun share lokaci suna tattaunawa da nufin kallon hanyar sake dawo da zaman a lafiya a kasashen Togo da ke tsakiyar rikicin siyasa dama Guinea Bissau da ta sake saka ranar zabe.
Ana dai kallon nasarar zabukan yankin da a baya ke zaman matattarar yan mulkin mulaka’u na iya kaiwa watanin da suka gabata su ga cigaban tattalin arziki dama zamantakewar al’umma.
Abun kuma da a cewar Mohammad Ibn Chambers dake zaman wakilin majalisar dinke duniya a yankin ke kara mata karfin gwiwa.
“Watannin baya an samu yin zabe cikin nasara a wasu kasashen yankin. Abun kuma da ya taimaka wajen kara ingantar nasarar da ake samu a cikin yankin ta tabbatar da tsarin demokaradiya a cikinsa."
Duk da cewar dai an nasarar yin zabuka a kasashen Mali da Saliyo a shekarar dake barin bankwana, shekarar dake tafe ma dai na kallon wasu zabukan guda biyu a tarrayar Najeriya dama Senegal da kuma yanzu haka ke daukar hankali.
To sai dai kuma a fada ta shugaban Najeriya Muhammad buhari da kuma ke jagirantar yankin yanzun, ba wani zabi face yin karbabben zabe a kasashen guda biyu.
“Kamar yadda muka sani Najeriya da kasar Senegal zasu gudanar da zabuka a watan Fabrairun badi, a nawa banagren tuni nayi alkawarin yin zabe a cikin zaman a lafiya kuma ingantacce."
Haka ita ma hukumar zabe da jami’an tsaro da ragowar masu ruwa da tsaki sun nuna aniyarsu ta yin zaben da babu tada hankali da nunin yatsa domin cika burin bukatun kasar.
Abun jira a gani dai na zaman irin nasarar ake gani cikin kasa a tsakanin na kasashen dake fatan cigaba amma kuma ke kallon matsalar tsaro da rashi na zaman a lafiya.