ECOWAS za ta yi taro kan Nijar
July 28, 2023Talla
Fadar shugaban Najeriya wanda shi ne ke jagorantar kungiyar ta ECOWAS ita ce ta sanar da haka. Kungiyar ta ECOWAS ta na shirin daukar mataki a kan nijar din. A karon farko tun bayan juyin mulkin da ya yi sabon jagoran mulkin sojin na Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya yi jawabi a gidan telbijan da rediyo na kasar inda ya bayyana dalilansu na yin juyin mulki.