Birtaniya na gab da barin kungiyar EU
January 29, 2020Talla
A kalaman su na bankwana sun gargadi Birtaniya cewa kada ta bijiro da wasu ka'idoji na son zuciya a game da sha'anin kasuwanci da sauran mambobin kungiyar ta EU.
Shugabar hukumar zartarwa ta EU Ursula von der Leyen, ta yi jawabi mai motsa zukata inda ta ce "ba zamu taba daina son ku ba kuma ba za ku yi mana nisa ba" wannan jawabi na Von der Leyen ya ratsa zukatan 'yan majalisar inda har sai da wasu daga cikin su suka zubar da hawaye.
Birtaniya dai ita ce kasa ta farko da zata fice daga kungiyar EU. A ranar Juma'ar nan da ke tafe da misalin karfe sha daya na rana za a kawo karshen batun Brexit da aka kwashe shekaru hudu ana kai ruwa rana a kansa.