1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Birtaniya sun cimma matsaya kan Brexit

October 17, 2019

kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya sun bayyana cewa sun cimma matsaya kan ficewar Birtaniya; sai dai nasarar za ta dogara ne da sahalewar majalisun Turan da Birtaniya.

https://p.dw.com/p/3RSO0
Belgien Brüssel EU Gipfel | Boris Johnson und Jean-Claude Juncker
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Kungiyar EU da Birtaniya sun cimma kudurin ficewar Birtaniya ne bayan ganawar shugaban EU Jean Claude Juncker da Firaiministan Birtaniya Boris Johnson a birnin Brussels da ke kasar Beljiyam. Yarjejeniyar dai za ta tabbata ne kawai idan aka kammala wajiban da za su sami sahalewar majalisar Turai da kuma ta dokokin Birtaniya.

Tun da fari dai mai shiga tsakani kan batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turan, Michel Barnier, ya bayyana kwarin gwiwar yiwuwar hakan a ranar 31 ga watan na Oktoba. Mr. Barnier yayin bayyana kalaman, ya kuma bukaci 'yan majalisar dokokin Birtaniya da su yi abin da ya dace lokacin kada kuri'a kan amincewa ko akasi kan yarjejeniyar da aka sabonta.

A ranar Asabar da ke tafe ne dai Firaiministan Birtaniya Boris Johnson zai sake bayyana a gaban majalisar dokoki kan batun.