EU: Gaza cimma matsaya kan matsalar makamashi
October 20, 2022Talla
Yawancin kasashen Turai sun yi kira da a iyankance farashin iskar gas, sai dai hukumar tarayyar Turai ta ce ba a bukatar hakan har sai tashin farashin makamashin ya kai kololuwa. Jamus da wasu kasashen sun nuna shakku kan matakan da zai shafi farashin, kana sun nuna damuwar cewa rage farashin ka iya haifar da matsala ga wadatar shi.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Firanministan kasar Hungary Victor Orban, wanda kasarsa ta dogaro kacokan kan makamashi daga Rasha ya ce, hukuncin da EU din ke shiri daukar tamkar sanya takunkumi ne ga fanin makamashin kasar.