Tarayyar Turai ta yi gargadi ga China
June 4, 2019Chinan dai ta murkushe masu bore da zanga-zanga da mahukuntan kasar suka yi a dandalin Tiananmen place mai cikakken tarihi da ke Peken. Ko baya ga kakkausar sukar da kungiyar ta EU ta yi wa Chinan kan ci gaba da dakile batun da hukumomin Peken ke yi game da wadanda sojojin kasar suka hallaka, kungiyar ta Tarayyar Turan ta yi kira da kakkausar murya ga gwamnatin ta China da ta gagauta sallamar duk wadanda ake tsare da su da suka hada da Lauyoyi da masu kare hakin dan Adam da China ta yanke wa hukuncin dauri tun a watan Yuni na shekarar 1989.
A wata sanarwa da babbar jami'ar diflomasiyar kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta wallafa ta ce, duk da yake a yanzu shekaru 30 da suka gabata da aikata kisan ga masu zanga-zangar, har yanzu hukumomin China sun ki sakin mara ga batun 'yancin fadar albarkacin baki da walwalar jama'a, lamarin da ta ce abin kokawa ne matuka.