EU: Haramcin safarar makamai a Libya
February 18, 2020Bayan tsawon lokaci suna muhawara a Brussels ministocin EU sun amince da kudirin kafa rundunar kiyaye safarar makamai a Libya. Bayan ganawa da takwarorinsa ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya sanar da cimma yarjejeniyar.
Matakan sun hada da sintirin jiragen sama da na ruwa. Sai dai wasu masu sharhi sun ce matakin ba zai kawo wani sauyi na azo a gani ba.
A shekarar da ta gabata aka dakatar da aikin rundunar da aka yi wa lakabi da "Operation Sophia" bayan da kasar Italiya ta baiyana adawa da cewa jiragen ruwan EU na kwaso 'yan gudun hijira da suka shiga halin tasku a kan teku ta sauke su a tashoshin ruwan Italiyar.
A baya bayan nan ma sai da gwamnatin Austria itama ta nuna adawa da sake farfado da rundunar sintirin akan teku tana mai cewa zai kara kwararowar 'yan gudun hijira zuwa kasashen Turai.