Turai na yin nazari kanmatsalar makamashi
December 15, 2022Talla
Shugabannin na yi kokarin ganin an mayar da martani bai daya don taimaka wa masana'antunsu a kan matsalar makamashi da yakin Ukraine ya haifar da kuma neman tallafin Amirka. Kasashen na Turai na son shawo kan Amirka da ta kawon kawancensu dauki, a daidai lokacin da ake fama da yaki a kan iyakokin tarayyar. Moscow ta rage yawan iskar gas zuwa ga kungiyar EU da kashi 80 cikin 100 tun bayan fara kai hare-hare a cikin watan Fabrairu da ya gabata.