1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Sabuwar manufa kan 'yan gudun hijira

Ramatu Garba Baba
September 23, 2020

Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar da sabuwar manufa kan 'yan gudun hijira tare da fatan yin raba daidai wajen karbar 'yan gudun hijira a tsakanin kasashe membobinta.

https://p.dw.com/p/3itzN
Belgien Brüssel | Pressekonferenz Migrationspakt | EU-Kommission
Hoto: Dursun Aydemir/picture-alliance/dpa

An jima ana kai ruwa rana kan batun rarraba dubban 'yan gudun hijira a tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai ba tare da cimma nasara ba, akwai kasashen da suka nuna rashin amincewa da tsarin kamar kasar Poland wadda ta yi fatali da bukatar karbar  'yan gudun hijirar. Dominik Tarczynski dan majalisar Kasar ne, ya ce ko dan gudun hijira guda ba za su karba ba matukar bai cika dokar kasa da kasa ba.

Dominik Tarczynski MEP
Dan majalisar Turai Dominik TarczynskiHoto: picture-alliance/Zuma/G. Banaszak

''Ba za mu amshi ko da dan gudun hijira guda ba muddun bai cika sharadin dokar kasa da kasa da ta ce idan mutum ya sami kansa cikin bala'i har ta kai dole ya tsere daga kasarsa ta asali, an nemi ya yada zango a kasar da ke makwabtaka da kasarsa don neman mafaka.''

Sai dai akwai wadanda ke ganin akwai siyasa kan wannan batun a daidai lokacin da 'yan gudun hijira ke cikin kunci musanman bayan gobarar da aka samu a sansanin Moria na kasar Girka, Anna Wilczynska kwararriya ce da ke nazari kan kaurar jama'a.

''Abu ne mai sauki a tsorata mutum a game da abin da bai sani ba, a yi ta surutu kan 'yan gudun hijira don a sami kuri'u a lokacin zabe ai shiri ne na son samun karfin iko a fagen siyasa''

Ursula von der Leyen's Rede zur Lage der EU
Shugabar hukumar EU Ursula von der LeyenHoto: AFP/J. Thys

Baya ga kasar ta Poland, akwai wasu kasashe da basu yarda cewa rarraba 'yan gudun hijirar ita ce mafita ba duk da yadda kungiyar Tarayyar Turan ke ci gaba da matsa kaimi. Shugabar hukumar tarayyar Turai ta EU Ursula von der Leyen, ta ce ba ja da baya har sai an cimma buri na magance matsalar

"Ba batun kasashe mambobi su bayar da goyon baya ko tallafi kadai bane, amma ta ya za su taimaka, Moria darasi ne saboda haka dole mu nemi mafita kan matsalar ‘yan gudun hijira kuma nauyin ya rataya a wuyanmu baki daya, saboda haka kungiyar Tarayyar Turai za ta tsaya tsayin daka don magance matsalar cikin hanzari''

A yayin da takaddamar ke ci gaba, kungiyar na son ganin an soke dokar da ke rataya nauyin dan gudun hijira kan gwamnatin kasar da ya fara sanya kafa, kasashen Girka da Italiya da suka kasance hanyar da ake bi don shiga turan sun ce ba a yi musu adalci ba.