1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Shirin sake farfado da tattalin arziki

July 18, 2020

Shugaban majalisar Turai Charles Michel, ya gabatar da wata sabuwar shawara a kan shirin sake farfado da tattalin arzikin kasashen kungiyar EU da cutar corona ta yi wa lahani.

https://p.dw.com/p/3fXN5
EU-Sondergipfel zur Bewältigung der Corona-Wirtschaftskrise
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/S. Lecocq

A wani zaman da aka kwashe sa'o'i 14 ana musayar yawu, taron ya sauya fasalin lamura tsakanin ba da rance da kuma tallafi, batutuwan da dama ake da bambancin ra'aya a kansu.

Shawarar Mr. Michel dai ita ce daga cikin euro biliyan 750 din da za a yi amfani da su, euro biliyan 450 za su kasance tallafi, yayin da ragowar 350 kuwa za su kasance kudade na rance.

A baya ya bayar da shawari ne na yin amfani da euro biliyan 500 a matsayin tallafi, sai kuma euro biliyan 250 a matsayin rance.

Wannan sabon tsarin dai ba zai yi wa kasashen Denmark da Sweden da Holland da kuma Austria dadi ba, saboda bukatarsu ta a bayar da kudaden a matsayin rance ba tallafi ba.