SiyasaJamus
EU ta amince da wani rigakafin corona
January 29, 2021Talla
Hukumar ta yi na'am da maganin na AstraZeneca ne a lokacin da ake kokarin ganin an maganta jinkirin samun maganin kanda garkin cutar ta corona a kasashe mambobin kungiyar EU.
Yanzu alluran corona uku ke nan aka amince da su a tsakanin kasashen, wadanda suka hada da na kamfanin Pfizer da Biontech da Moderna da kuma ta AstraZeneca.
Tuni aka yi odar sabon maganin miliyan 300, wanda aka yi ittifakin cewa yana da sauki ta fuskar kudi da kuma adana.
Akwai ma karin wasu alluran miliyan 100 da kasashen za su sake oda nan ba da jimawa ba.