1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: EU ta bude iyakoki ga wasu kasashe

Abdullahi Tanko Bala
June 30, 2020

Kungiyar tarayyar Turai a wannan talata ta amince da bude iyakokinta ga wasu kasashe 15 amma banda Amirka yayin da aka sami karuwar annobar corona da ta hallaka mutane fiye da 500,000 a duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3ebNK
Spanien Coronavirus Grenzöffnung
Hoto: Reuters/A. Gea

Bude iyakokin da tarayyar Turai ke yi sannu a hankali na zuwa ne yayin da kasashe ke kokarin farfado da harkokin tattalin arzikinsu a waje guda kuma suke daukar matakan yaki da sake barkewar annobar ta COVID 19 wadda ke cigaba da yin kamari a kudancin Amirka da ita kanta kasar Amirka da Rasha da kuma Turkiyya.

Jadawalin kasashen da aka bude wa iyakokin sun hada da Aljeriya da Ostireliya da Kanada da Jojiya da Montenegro da Maroko da New Zealand. Sauran su ne Ruwanda da Sabiya da Koriya ta Kudu da Thailand da Tunisiya da kuma Yurugai.

Matafiya da suka fito daga Chaina inda cutar corona ta fara bulla a bara za a bari su shiga kasashen Turai ne bisa sharadin Beijin itama za ta bude iyakokinta ga yan kasashen Turai.