1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Allurar rigakafi don yaki da mura

July 15, 2020

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun bukaci kasashen da ke cikin kungiyar su kaddamar da gagarumin shirin allurar rigakafin masassara domin rage hadarin yaduwar cuttukan mura da kuma corona a kakar bana.

https://p.dw.com/p/3fN7O
Krankenschwester mit Spritze
Hoto: picture-alliance/dpa/I.Zarembo

Hukumar tarayyar Turan na fatan kawar da yiwuwar sake cushewar asibitoci da marasa lafiya kamar yadda aka gani lokacin kololuwar yaduwar annobar corona a nahiyar Turai a tsakanin watan Maris da Aprilu.

Mataimakin shugaban hukumar tarayyar Turan Margaritis Schinas, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen turan su sayi karin magungunan mura su kuma tabbatar da cewa an yiwa mutane da dama allurar rigakafin.

Hedikwatar tarayyar Turan a Brussel na son ganin gwamnatoci sun yi amfani da manhajar gano mutane da ke dauke da cutar corona, sai dai kawo yanzu kasashe goma ne kacal daga cikin kasashe 27 na tarayyar Turan suke amfani da manhajar.