Turai ta kakkabawa Rasha sabbin takunkumai
February 22, 2021Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ya fada wa manema labarai jim kadan bayan kammala taron da suka yi a birnin Brussels cewa, ba su da zabi face daukar matakin sanya takunkumin. Sa-in-sa tsakanin bangarorin biyu dai, ya biyo bayan kama jagoran adawa Alexei Navalny kuma mai caccakar gwamnatin Shugaba Vladimir Putin, bayan da ya dawo daga jinyar da ya yi a Jamus a sanadiyar gubar da aka sanya masa.
Kungiyar EU mai mambobin kasashe 27, ta kuma sanya takunkumi ga wadanda ke da hannu a sanya wa madugun adawar guba, sai dai Lauyan Navalny ya bukaci a sanya musu takunkumin tafiye - tafiye da toshe asusun ajiyar manya 'yan siyasa da ke zama na hannun daman Shugaba Vladimir Putin. Kotu a kasar ta yanke wa Navalny hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da rabi.