Tarayyar Turai na shirin aika sojojinta a Mozambik
June 30, 2021Talla
Wata majiyar diflomasiyar kungiyar EU da ta tabbatar da labarin ta ce dakarun za su yi aikin horas da sojan Mozambik ne dubarun yaki da 'yan ta'adda, kana kuma sai nan da gaba ministocin harkokin wajen kungiyar za su tabbatar da matakin. Tuni dai kasashen Faransa da Spain da Italiya da Luxemburg suka bayyana anniyarsu ta tura nasu dakarun, biyo bayan bukatar hakan da kasar Portugal ta nuna tun a cikin watan Maris, kwanaki bayan wani mummunan harin 'yan bindiga a birnin Palma mai arzikin gas da ke dab da gabar tekun kasar. A na su bangare u ma jagororin kungiyar raya tattalin arzikin yankin gabashin Afirka, sun cimma matsaya na aike da wata bataliyar sojojin su a yankin da nufin kakkabe mayakan.