1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Fada tsakanin Kurdawan SDF da na Turkiyya ta halaka mutane

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 5, 2025

Kurdawan SDF sun rasa mayaka 85 a fadan, yayin da tsagin da ke samun marawar dakarun Turkiyya ya rasa mayaka 16.

https://p.dw.com/p/4oppm
Dakarun Kurdawan SDF na Syria
Hoto: Orhan Qereman/REUTERS

Tsananin fada tsakanin Kurdawan kasar Syria wato SDF dake samun goyon bayan Amurka, da kuma tsagin da ke samun goyon kasar Turkiyya, ya yi sanadiyyar mutuwar mayaka sama da dari daga bangarorin biyu a kasar Syria, kamar yadda kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights ta sanar ranar Lahadi.

Karin bayani:Siriya ta yi sulhu da kungiyoyi masu dauke da makamai

Kurdawan SDF sun rasa mayaka 85 a fadan, yayin da tsagin da ke samun marawar dakarun Turkiyya ya rasa mayaka 16, bayan shafe tsawon kwanaki biyun da suka gabata suna gwabzawa a arewacin Syria ta sama da ta kasa, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da sauran makaman yaki.

Turkiyya dai na kallon kurdawan a matsayin wani bangare na 'yan tawayen PKK da take yaki da su tun cikin shekarun 1980.

Karin bayani:Yan sandan Jamus far wa Kurdawa yan Iraqi masu safarar baki

Yanzu haka dai 'yan tawayen HTS masu samun goyon bayan Turkiyya ne ke rike da kasar Syria, bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a farkon watan Disamban shekarar 2024 da ta gabata.